Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wa Ke Da Hakkin Hoton "Selfie" Biri Ko Mutun?


Biri Mai Daukan Kanshi Hoto
Biri Mai Daukan Kanshi Hoto

Masu iya magana kan ce, “idan har kana da rai, to zaka ga abubuwa” al'ajabi.A jiya ne wata kotu a jihar San Francisco ta kasar Amurka, ta saurari wata kara da wani mutun mai suna David Slater, ya shigar. Mr. David, dan kasar Ingila ne, kuma sana’ar shi itace daukan hotunan musamman na dabbobin daji.

Mr. David, dai ya bakunci wani tsibiri da ake kira “Sulawesi” a kasar Indonesia, inda ake zuwa don kallon namun daji, ya shirya Kyamarar daukan hoton shi, dai-dai da kawai idan aka taba abun daukar hoton, zata dauka batare da bata lokaci ba. Sai ya ajiye kusa da wani “Biri” mai suna “Macaque” Birin bai yi wata-wata ba, yana zuwa wajen kyamarar sai yayi dace ya taba wajen daukar hoto, sai ga biri ya dauki kanshi hoto.

Hukumar kare hakkin dabbobi ta Amurka, suna jayayya da Mr. David, da cewar daga shi har Birin babu wanda ke da hakkin rike wannan hoton, domin bashi ya dauki hoton ba, birin ya dauki kanshi-da-kanshi.

Shi kuwa Mr. David, yace ai badan ya dai-dai ta kyamarar tashi ba, wanda har birin ya taba kuma ya dauka, ai kuwa da birin ba zai iya samun damar daukan hoton ba, don haka shike da hakki a kan hoton. Duk dai abun da ya kawon wannan takaddamar shine, an saka hoton wannan birin a cikin littafin dabbobi wanda ake siyarwa. Wanda Mr. David ke ganin yakamata a nemi izinin shi kamin a sa hoton.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG