Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Karamar Hukuma Don Al'umma


Matasa
Matasa

Sanin kowa ne cewar gwamnati kananan hukumomi an kirkire sune don sune sukafi kusanci da talakawa, kuma baban aikin su shine su tai makama al’umarsu a kowane hali suka samu kansu. Wasu matasa masu sana’ar gwari suna fuskantar tirjiya daga hukumomi, dangane da wani guri da suke samu suna yin sana’arsu.

Al’uma unguwar Dorayi Charanci, na mika koken su ga hukumomi da su dubi Allah su taimaka musu ganin cewar sun dauki lokaci mai dama suna gudanar da sana’ar su a wannan yankin, kuma babu wata damuwa. Amma sai gashi jiya anbasu takardar cewar ba a da bukatar ganin wani a wannan yankin ya na gudanar da sana’a.

Wanda wannan zai iya jefa wasu da dama cikinsu cikin halin ha’ula’I, don kuwa wasu daga cikin su basu san yadda zasuyi ba, idan aka tashe su daga wannan wuri. Don haka sun a mika kukansu ga Allah kuma da hukuma su taimaka musu don kada su shiga cikin halin lahaula.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG