Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kayan Gwanjo na Tallafawa Rayuwar Matasa


Usman Mohammed, mai sana'ar sayarda Jaka bayan ya tashi daga makaranta a Kano
Usman Mohammed, mai sana'ar sayarda Jaka bayan ya tashi daga makaranta a Kano

Ba ‘yayan masu hannu da shuni ka dai kan iya kawo chanji a cikin al’umah ba, kowa kan iya bada tashi gudunmawa a kowane irin bangare na rayuwa. Babban abun sha’awa a nan shine, yakamata asamu wadanda zasu dinga bama yara matasa shawarwari a lokacin kuruciyarsu.

A irin yunkuri na tallafawa tattalin arziki da neman zama wani abu a rayuwa wani matashi mai suna Usman Muhammad ya dauki sana’ar sayo kayan gwanjo da kuma tallata su ga masu karamin karfi, wanda tahaka ne shima yake samun abun tsare lalura ta yau da kullun. Abun sha’awa da wannan matashin shine, ya kanje makaranta wanda idan ya dawo sai ya fita neman abun da zai yi makanshi lalura batare da ya dogara da iyayenshi ba, duk dai da cewar shi wannan matashi almajiri ne da ya baro iyayen shi a garinsu. Abun la’akari da shi anan shine wai wane yunkuri al’umah sukeyi wajen sa yaransu hanya da ta dace, da koya musu sana’a tun da yarintar su.

Yakamata ace yara matasa suyi koyi da wannan yaron wajen samun sana’ar da zasu yi dogaro da kansu batare da sun jira wani ba, kuma kada su raina sana’a koya take. Haka kuma yakamata ace kowane yaro ya zamana yana da burin zama wani abu a rayuwa, kada su sama kansu mutuwar zuci, su kuma sani cewar babu abun da zaka zama a rayuwa idan baka sa kanka a ciki ba, haka kuma duk abunda wani yazama a rayuwa ba kawai rana daya ya tashi yazamo ba, sai da yayi kokarin sa, tunda yarinta wanda daga bisani ya cinmma burin sa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG