Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kek Abincin 'Yan Gayu ga Talakawa


Kek
Kek

Kek wani abincin kwalama ne wanda ba kowa ke damuwa da yaci ba, saboda shi wani abune mai wahalar yi, don haka yasa yake da tsada. A al’ada irin ta wasu kasashen duniya, kek abinci ne da duk lokacin da aka kamala cin abinci a kanci. A al’adun su cin kek wani abun jin dadi ne koma babu yadda za’ayi aci abinci ba’a ci kek ba.

Tabbas a kasar Najeriya, sana’ar yin kek wata sana’ace mai wuyar sha’ani don tanada wahalar yi. Amma a wajen Naja’atu Salisu Alhasan Bichi, wanna wata sana’ace da take ganin lallai tana da sha’awar ta don haka duk wahalar dake ciki bata gani, musamman ma idan zata samu abun da zatayi lalurorinta na yau da kullun batare da ta yi karamar murya ba. Wannan sana’ar ta yin kek ba kawai don samun abun hannu take yin ta ba, harma da taimakama al’uma don su samu cin abun marmari da kuma gina jiki a cikin sauki, wanda ba lallai sai masu hali kadai zasu iya cin wannan kayan dadin ba.

A kuma bangare daya, wannan sana’ar tata, ta tai maka mata matuka, tunda har bata tambayar mijinta abun lalura, ko roko wajen wasu dangi. Babban abun da yakamata ace mata matasa su maida hankali shine suyi kokarin samun sana’a da take mai tsafta da ban sha’awa, wadda bakowa ke iyayin taba duk wahalar ta su sa kansu, don tahaka ne kawai za’a yawaita dogaro da kai batare da an jira wani ba.

Ta kara kira da mutane kada su rena sana’a koya take, don hakuri da juriya sune maganin kowace irin rayuwa, to yakamata kowa ya mike wajen tallafawa tattalin arzikin kasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG