Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masoyin Kasar Amurka ya Baro Garin Kumo Zuwa Abuja a Kafa


Masoyin Kasar Amurka
Masoyin Kasar Amurka

Kowane dan adam da bukin zuciyar shi, wani matashi Usman Yari, ya bayyanar da kaunarsa a fili da yake ma kasar Amrka. Wannan matashin dai ya nuna cewar yakasance me kaunar wannan kasar ne tun yana yaro, kuma ganin cewar wannan kasa me kaunar kasar Najeriya ce yasa yakara kaunarta da kuma irin yadda take taima kama kasashen duniya musamman ma kasar Najeriya.

Ya bayyanar da dalilin yin wannan tattaki nashi daga garin Kumo a jihar Bauchi, zuwa babban birnin tarayya Abuja, don taron baki da zasu zo don taya murna da kuma rantsar da sabon shugaban kasa da za’ayi nan da ‘yan kwanaki kadan. Shi dai bababan abun da yasa yake wannan tattaki shine, don nuna nashi jindadin da yadda wadannan kasashen ke nuna soyayyar su ga zababben shugaban kasar Najeriya Ganaral Muhammadu Buhari, mai murabus.

Yana kuma fatar Allah yasa wadannan kasashen zasu ba ma shugaban kasar hadin kai da duk wani taimako da zai bukata don gudanar da mulkinshi a kasar baki daya. Ya kara da cewar don Allah mutane suyi kokarin su bama wannan gwamnatin mai zuwa duk wani gudunmawa da yakamata don cin nasarar, wanda nasarar kasar nasarrar kowane a kasar baki daya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG