Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Senegal Ta Doke Ghana Da Ci 2-1


Mame Birame Diouf, na biyu a hagu, yana jefa kwallon Senegal na farko a ragar 'yan Ghana
Mame Birame Diouf, na biyu a hagu, yana jefa kwallon Senegal na farko a ragar 'yan Ghana

Senegal ta doke Ghana da ci biyu da daya a wani wasan da ya burge kowa a gasar cin kofin kasashen Afirka, a bayan da dan wasan Senegal da ya shigo daga baya, Moussa Sow, ya jefa kwallo na biyu a daidai lokacin da alkalin wasa ke shirin hura tashi.

Sow ya narka wannan kwallo na biyu a bayan da tun farko Mame Biram Diouf ya ramawa Senegal kwallon bugun fenariti da Andrew Ayew ya jefa cikin raga kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Wannan sakamakon babban abin dama-lissafi ne ga tsohon manajan Chelsea, Avram Grant, a wasansa na farko a zaman kwach na kasar Ghana. Yanzu kasar Ghana ta shiga hali na tsaka mai wuya a kokarin hayewa zuwa zagaye na biyu daga wannan rukuni nasu.

XS
SM
MD
LG