Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Liverpool Na Son Saye Alex Song, Man U Kuma Ta Ki Bada Hayar Adnan Januzaj


Alex Song, wanda FC Barcelona ta bayarda hayarsa ma West Ham United
Alex Song, wanda FC Barcelona ta bayarda hayarsa ma West Ham United

Jita-jita dai ba ta karewa a fagen tamaula. Wata gaskiya, wata kuma,ba sosai ba.

Liverpool ga misali an ce tana son mika tayin Fam miliyan 11 da rabi domin sayen Alex Song. Liverpool din tana kokarin doke Manchester United da ma kungiyar West Ham inda aka bayarda hayar Song domin maida shi dan wasanta na dindindin. Asali dai Alex Song dan wasan FC Barcelona ne.

A wani gefen, har yanzu Robin van Persie bai soma tattauna sabon kwantaraki da Manchester United ba, duk da cewa saura watanni 18 kwantarakinsa na yanzu yak are. Akwai alamun zai sauya sheka ke nan ko yaya?

Har yanzu a Manchester United, manajanta Louis van Gaal ya those kokarin da kungiyar Genoa ta kasar Italiya ta yin a hayar Adnan Januzaj mai shekaru 19 da haihuwa daga Man U.

A nan kusa da Amurka, akwai rade-radin cewa Miroslav Klose zai bar Lazio domin ya komo nan Amurka da nufin bugawa a wasannin lig-lig na Amurka da ake kira MLS. Yanzu dai an tabbatar da cewa ba zai yiwu ya koma kungiyar Werder Bremen ta Bundesliga a Jamus ba.

XS
SM
MD
LG