Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Cikin Firij Aka Sanya Bam Da Ya Fashe A Kano


Harin bam na ranar 19 Mayu a Sabon gari a Kano

Hukumomi a Kano sun tabbatar da cewa wata mace guda daya ta mutu, yayin da mutane 8 suka ji rauni a lokacin da wani abu mai kamar bam yayi bidniga a wata tashar motar safa dake New Road a Unguwar Sabon gari.

Kwamishinan 'yan sandan Jihar Kano, Adelere Shinafa, wanda yayi tattaki zuwa wurin da wannan lamarin ya faru, ya shaidawa 'yan jarida cewa wannan abu ya fashe ne a lokacin da ake lodin kaya cikin wata mota mai zuwa Fatakwal.

Yace wannan abu ya fashe ne cikin wata na'urar firij, a saboda haka su na kyautata zaton cewa an saka nakiya ko bam ne cikin wannan firij, ya kuma tashi a lokacin da ake lodinsa a cikin motar.

Wannan shi ne karo na biyu da ake kai hari a wanna tashar mota a Kano.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG