Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Tashi A Kano Yau Alhamis


Lokacin da bam ya tashi a hedkwatar 'yan sandan Kano a ranar 20 ga watan Janairun 2012

Rahotanni daga Kano na cewa wani abu ya fashe a cikin tashar motar Sabon Gari, inda ake lodin fasinja akasari zuwa jihohi da biranen dake kudancin Najeriya.

Har yanzu babu rahoto na mutuwa ko rauni daga tashin wannan abu da ake kyautata zaton bam ne.

Wasu kafofi sun ce an shiga da wannan abu ne a cikin jaka, amma ba a san ko an ajiye jakar aka tayar da ita daga nesa ne ko kuma harin na kunar bakin wake ba ne.

An sha kai hare-haren bam a kan wannan tasha, inda akasarin mazaunanta da masu amfani da ita, 'yan asalin wasu jihohin kudancin Najeriya ne.

Kwamishinan 'yan sanda na Jihar Kano yana can wurin da abin ya faru, kuma zamu kawo muku karin bayani.

XS
SM
MD
LG