Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisa ta Bukaci Cif Joji Ya Kafa Kwamitin Tsige Nyako


Murtala Nyako, gwamnan Jihar Adamawa
Murtala Nyako, gwamnan Jihar Adamawa

Majalisar dokokin jihar Adamawa, ta zartas da takardar bukatar mai rikon mukamin cif jojin jihar da ya kafa kwamitin da zai binciki gwamna Murtala Nyako da mataimakinsa Bala J. Ngilari, da nufin tsige su.

Majalisar ta ce tana da hurumin yin hakan a saboda gwamnan bai amsa takardar tuhumarsa da aikata laifuffuka da ta wallafa cikin jaridu ba, duk da cewa kotu ta ba da umurnin kada ayi hakan.

Sai dai kuma kakakin gwamnan, Ahmad Sajoh, yace wannan matakin bai tayar musu da hankali ba idan dai za a yi aiki da doka, domin babu wanda ya gabatarwa da gwamna Nyako takardar tuhuma.

Akwai mutane da dama dake zargin cewa yunkurin tsige gwamnan daga kan kujerarsa ya taso ne tun daga Abuja.

Majalisar Dokokin Adamawa ta Bukaci Cif Joji Ya Kafa Kwamitin Tsige Nyako - 2'06"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG