Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Daukar Kaya Ya Fadi Ya Kashe Mutane 4 Dake Cikinsa


jami'an tsaro su na kokarin cire gawarwaki daga jirgin daukar kaya da ya fada kan wani gini, laraba 2 Yuli a Nairobi, babban birnin Kenya
jami'an tsaro su na kokarin cire gawarwaki daga jirgin daukar kaya da ya fada kan wani gini, laraba 2 Yuli a Nairobi, babban birnin Kenya

Wani jirgin saman jigilar kaya ya fada kan wani gini a Nairobi, babban birnin Kenya, ya kashe mutane 4 dake cikinsa.

Jirgin ya abka kan wannan gini mai hawa biyu dake kunshe da kananan kantuna jim kadan a bayan tashinsa yau laraba da safe daga babban filin jirgin saman Nairobi.

Jirgin ya kama da wuta, inda ya rusa tare da kona wani bangaren ginin da ya fada kai. Masu bincike suka ce watakila jirgin ya kara da wayar wutar lantarki kafin ya fadi kan ginin.

Jirgin yana dauke ne da wani ganye mai suna "Khat" zuwa kasar Somaliya. Khat dai yana da dangantaka da goro.

XS
SM
MD
LG