Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Wasannin NPFL Suka Kasance


Ranar lahadi 25, ga watan satumba 2016, an fafata wasanin mako na 37, inda ya rage saura mako daya tak a karkare duka wasannin.

Ga yadda wasannin suka kaya

River 0-0 Abia warriors

Niger Tornadoes 3-1 MFM

Ifeanyi Ubah 1-0 Enyimba

Nasarawa United 2-2 Akwa united

Shooting Star 1-0 Wikki tourist

Sunshine 1-0 Warri Wolves

Ikorodu united 1-2 Enugu Rangers

El-kanemi 1-0 Plateau United

Heartland 1-0 Kano Pillars

Kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers tana dab da lashe gasar Nigerian professional football league ta shekarar 2016, inda take kan gaba da maki 60 sauranta wasa guda daya da zata buga a gida tsakaninta da El-kanemi ranar 2/10/2016.

Rivers united na mataki na biyu da maki 57, ita kuwa zata karkare wasanta ne a waje tsakaninta da Akwa united ranar 2/10/2016.

Ifeanyi Ubah na mataki na uku da maki 56, kuma zata kammala wasanta a waje ne da MFM ranar 2/10/2016.

Yayinda Wikki tourist take mataki na Hudu da maki 54, zata karasa wasanta a gida tsakaninta da Sunshine ranar 2/10/2016.

A kasan tebur kuwa, Warri wolves na mataki na sha takwas da maki 42

Ikorodu na mataki na sha tara da maki 32, sai Giwa da aka dakatar da ita ta na mataki na ashirin ba tare da maki ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:08 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG