Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alhaji Ya Yiwa Wata Yarinya Marainiya Ciki


Ana zargin wani mai suna Alhaji Giwa, mazaunin kauyen Birnin ruwa a jihar Sokoto, da yiwa wata yarinya marainiya mai suna Maimuna, fyade wanda kuma yayi sandiyar ta na samu juna biyu.

Wani ma’aikacin gidan rediyon muryar Jamus, Faruk, Muhammad Yabo, kamar yadda ya ruwaito a shafinsa na facebook, yayi zargin cewa Alhaji Giwa yayi watsi da Maimuna.

Yabo, ya kara da cewa an kai Alhaji Giwa, kotun shara’a, a jihar inda ya musanta zargin.

Wasu shedu sun fadawa kotu cewa wanda ake zargin yayi alkawarin zai kai Maimuna asibitin kwararru domin a zubar da cikin amma daga bisani ya canja ra’ayi.

Maimuna dai yanzu tana da cikin wata takwas kuma daga dukkan alamu, Alhaji Giwa, ya musanta cewa shine ya yi mata,ita kuwa Maimuna ta ce ita bata san kowa ba sai Alhaji Giwa.

XS
SM
MD
LG