Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Kun San Alfanun Da Jikin Dan Adam Ke Samu a Lokacin Barci?


Wata tana rintsawa a zaune
Wata tana rintsawa a zaune

Wani bincike da masana suka yi kan yadda dan adam ke barci, ya nuna alfanun da ke samun sassan jikin bil adama a duk lokacin da yake suke barci.

Me ka sani dangane da irin halin da jikinka yake yi a daidai lokacin da mutun yake barci? Dr. Michael Breus, likitan kwakwalwar dan’ adam ne a wani asibiti mai zaman kansa a kasar Amurka.

Ya fitar da sakamakon wani bincike da suka gudanar, wanda yake bayyanar da wadansu abubuwa da jikin dan adam kan yi a daidai lokacin da yake barci.

A lokacin da mutun yake barci, dimin jikinsa kan sauka, inda ya kan yi sanyi.

Hakama duk a cikin barci mutum na rage nauyi, domin ruwan da ke jikinsa ya koma kasa don zama fitsari, haka numfashin da mutun kan yi yakan kara rage kitsen da ke jikin bil’adama.

A bangaren yara kuwa, a daidai lokacin da suke barci ne kasusuwan jikinsu suke kara mikewa, don kara tsawo da karfi.

A wannan lokacin, zuciya na samun hutu yadda ya kamata ta inda har jinin dan’adam kan sauka, haka ma, duk gabobin jiki suna mutuwa a wannan lokacin.

A lokacin da mutun yake barci, kwayar idonsa ta kan yi yawo fiye da idan baya barci, wanda hakan kansa mutun idan ya tashi daga barci ya ga kwantsa a idonsa.

Har ila yau, binciken ya bayyana cewa barci yana taimakawa wajen wanke duk wasu kananan cuttutuka da duk wata kura da ta shiga cikin ido da rana.

Haka ma, a lokacin da mutun yake barci, duk wasu jijiyoyin jikinsa kan mike wajen isar da jini a ko ina, wanda hakan ke taimakawa matuka wajen fitar da wasu cututtuka daga jikin dan’adam.

Har ila yau, fatar jiki na samun karin lafiya saboda gudanar jini da kuma iska mai inganci da ke shiga ta kafofin jiki.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG