Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Bukin Karrama Jarumai A Duniya Nishadi Ta Kannywood


Sadiq Sani Sadiq
Sadiq Sani Sadiq

Kadan kenan daga cikin shakatawar da aka gudanar a yayin bikin bada takardar girmamawa, ga wadanda ake sa ran fina-finansu ko wakokinsu sun cancanta da su samu lambar yabo a gasar AMMA, karo na biyar da za’a gudanar a garin Katsina.

An dai gudanar da wannan biki na bada lambar girma ne a jihar Kano Najeriya, inda wadanda suka samu takardar girmamawa ke tsammanin zasu lashe wannan kambi, na AMMA award a karo na biyar .

DandalinVOA dai ya samu zantawa da wasu daga cikin su inda muka soma da Sadiq Sani Sadiq wanda yace yana da yakinin zai lashe kambin.

Yace fim dinsa na Rai da Hakki ya taka rawar gani sosai. kuma shine babban jarumi a fim din, yace babu tantanba tunda ya samu yabo, to yana sa ran zai lashe wannan lambar yabon, kuma wannan ne karo na biyu, domin kuwa ya samu nasara a bara.

Shima Kabiru Jammaje, cewa yayi ya samu yabo a fim dinsa na (Light and Darkness) Haske da Duhu, wanda yake kunshe da sakon ilimi. Shi kuwa Galadima Muhammad, cewa yayi a wannan karon zasu barwa wasu su gwada ko zasu samu. Za'a dai gudanar da bikin karramawa a jihar Katsina.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG