Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rahoto Na Tabbatar Da Cewar Halittun Cikin Teku Na Fuskantar Barazana


Akwai tabbacin cewar, halittun cikin Teku zasu fuskanci matsala, sanadiyyar gurbatacciyar iska da ake samu daga rayuwar yau da kullun a cikin birane. Binciken da aka kwashe shekaru 8 ana gudanarwa da ya hada da manazarta kimiyya mutane 250.

Binciken ya tabbatar da cewar, halittu dake cikin teku bazasu dinga samun nagartacciyar iska da zata basu damar walwala ba, da kuma basu damar saka kwai da kyankyashe su cikin lafiya.

Hakan na nuni da cewar za’a samu karancin halitun cikin ruwa a nan da shekaru kadan masu zuwa, yawan ‘yaya ko kwai da halittun zasu dinga sakawa zai ragu matuka. Haka tsofaffi zasu dinga mutuwa batare da rayuwa mai yawa ba.

Sakamakon binciken ya tabbatar da cewar ana iya samun karancin hallitun ruwa da mutane kan iya ci, saboda matsalar rashin walwala ga halittun. Jiragen ruwa da ke shawagi a cikin teku suna kara taimakawa wajen karuwar gurbatar iskar da hallitun ke shaka.

A lokutta da yawa, jiragen ruwa kan fesa bakin mai cikin teku, hakan na shafar lafiyar ruwan da halitun ciki. Masanan na ganin sai an fito da wasu sababbin dubaru, don shawo kan matsalar tun kamun ta wuce inda aka santa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG