Mu’azu Muhammad, wanda aka fi sani da MM Haruna, malamin makaranta kuma darakta mai shiryar fina-finan Hausa ya kirkiri gasar wasa kwakwalwa ga wadanda suka kalli fim din da ya fitar a kwananan mai suna Hangen Nesa’.
MM Haruna, ya ce wasu daga cikin dalilan da suka sa suka ba da kyaututtuka ga wadanda suka kalli fim din “Hangen nesa” domin tababbatar da sakon da ke cikin fim din ya sami masu kallo tare da cusa masu akidar da fim din ya kunsa ta muhimmancin ilimi ga mata.
Ya ce a hannu guda fim din na nuni ne da bada kwarin gwiwa ganin ire-iren fina-finai masu alaka da hakan tare da fadakar da masu kallo akan abinda fim din ya kunsa , da sauran ilimomin da fim din ke dauke da su.
Ya kara da cewa fim din ya isar da sakonin ilimi da ma na siyasa domin samar da waraka ga yadda ake tafiyar da rayuwa a yanzu. MM Haruna, ya ce a gasa ko wasa kwakwalwar da ya shirya a kafar sadarwa ga wadanda suka amsa wasu tambayoyi da aka fitar dangane da fim din dai zai ankarar da mutane kan abunda suka kalla, sannan akalla mutane shidda ne suka ci wannan gasa, kuma kyaututtukan sun hada da atamfofi, agoguna da sauransu.
Daga karshe ya bayyana cewa gasar ta nuna cewar yadda aka amsa tambayoyin da akayi cewar sakon da ake son aikawa ya isa, sannan an samu nasara domin abinda ake so a cusawa al’umma ya isa duba da yadda suka bada amsosinsu.
Facebook Forum