Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalolin Zama Nesa Da Abokan Kauna


Masu iya magan sun ce ra'ayi riga!, kamar yadda muka saba a kowane karshen mako, shirin samartaka na dandalinvoa kan nemi jin ra'ayoyin matasa daban daban akan batutuwa daban daban da suka shafi rayuwa, zamantakewa, soyayya da makamantan su.

A wannan karon mun tattauna ne akan yanayin zama nesa da masoyi ko masoyiya, matar aure ko miji, a sakamakon aiki ko sana'a, kai harma yanayin haduwa da a lokuta da dama kan kasance haka

Idan ta kasance kowane daya daga ciki ya fito daga bangare mai nisa, ganawa kan zama da wahala sai dai da shike zamani ya samar da hanyoyin sadarwa da zama'a zasu iya amfani da su wajan magana da juna har ma suna iya ganin fuskokin juna a duk lokacin da suka so.

Domin karin bayani, saurari wannan garjerar tattaunawa akan irin matsalolin dake tattare da irin wannan yanayi da wasu kan sami kawunansu a sakamakon wasu dalilai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:09:30 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG