Shugaban kungiyar kwallaon kafa ta Super Eagles, Gernot Rohr, ya yi korafin cewa bashi da kwarin gwiwa da tabbacin gane adadin yawan shekarun kowane dan wasan kwallon kafa dake zama da kuma taka leda a gida Najeriya.
Rohr, ya bayyana cewa makasudin dalilin da yasa baya gayyatar ‘yan wasan domin bugawa babbar kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa ta kasa wasa kenan.
Da yake hira da kafar yada labaru ta Brila FM, mai horas da ‘yan wasan ya kara da cewa “ akwai dadaddiyar matsalar tantance yawan adadin shekarun ‘yan wasa a Najeriya, bamu iya gane yawan shekarunsu na ainihi” .
Kawo yanzu dai mai tsaron gida Ikechukwu Ezenwa, ne kadai dan wasa mai zama a Najeriya, Rohr, ya gayyata domin wasannin da zasu fafata da kungiyar kwallon kafa ta Algeria da Senegal.
Tsohon mai horas da ‘yan wasan kwallon kafa na kasar Gabon da Burkina Faso, ya kara da cewa har yanzu kofa a bude take domin kwararrun ‘yan wasan kwallon kafa na NPFL.