Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararru Su Na Mayarda Martani Ga Bidiyon Boko Haram Kan Daliban Chibok - 12/5/2014


Kwararru su na ci gaba da mayarda martani ga sabon faifan bidiyo na 'yan Boko haram, inda a ciki suke neman da a sako 'ya'yan kungiyar kafin su sako dalibai mata na Chibok da suka kama, inda suka nuna wasu daga cikin wadannan dalibai a bidiyon nasu.

A hoton bidiyon an ga yara mata kimanin 130 sanye da hijabi cikin wani jeji, kamar su na addu’a. A cikin bidiyon, madugun Boko Haram, Abubakar Shekau, yace an ‘yantar da yaran ta hanyar zamowa Musulmi. Yace ba za a sako su ba, har sai an sako mutanensu dake tsare.

Amma wani masanin tsaro kuma dan asalin jihar Borno, yace babu ta yadda za a iya alakanta mutumin da yayi kisa, da wanda ko balaga ma bai yi ba. Kwararren yace idan har za a sako 'yan Boko Haram da ba su aikata laifi ba ne, to ana iya duba wannan bukata domin a kawo karshen lamarin nan, amma kuma ba zai yiwu a ce a sake mutumin da ya aikata kisa, kuma doka ta hau kansa ba.

malamin yace su ma kansu 'yan Boko Haram sukan kashe ko hukumta mutanen da suke zargi da bayar da labarinsu ga hukumomi.
XS
SM
MD
LG