Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Farin Kaya a Najeriya Sun Haramta Zanga-zangar Lumana A Kaduna Da Kame Mutane Uku - 10/5/2014


Kakakin SSS, Marilyn Ogah
Kakakin SSS, Marilyn Ogah

NIGERIA - Yunkurin hadakar kungiyoyin mata da matasan da suka zaman dirshen domin nuna damuwarsu game da tabarbarewar tsaro a Najeriya ya samu cikas, biyo bayan haramta taron da hukumar jami’an tsaro Farin Kaya a Jihar Kaduna tayi.

Yanzu hukumar SSS din ta fito da makamai, tana barazanar harbin fararen hula masu aniyar gudanar da zanga-zangar lumana.

Da yake nuna damuwarshi game da wannan mataki, shugaban hadakar kungiyoyin da suka shirya wannan zama da dirshen Komrade Ibrahim Garba Wala yace an riga an kama wasu mambobinsu mutum uku.

“Abun takaici shine, jami’an tsaro sun hana mu gudanar da wannan abu. Sun gayyace mu zuwa Ofis dinsu, wanda muka gani cewa tamkar dama ce wadda zamu yi aiki dasu, jami’an tsaro saboda samawa al-umma da mu da muka fito, samun tsaron da ya kamata,” inji Ibrahim Wala.

XS
SM
MD
LG