Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bamu Manta Daku Ba ‘Yan Matan Chibok


Jiya Talata 'yan matan Chibok su dari biyu da goma sha tara suka cika shekara daya a hannun 'yan Boko Haram.

Yau shekara daya cur ke nan da ‘yan kungiyar Boko Haram suka farma makarantar ‘yan mata dake garin Chibok cikin jihar Borno suka kwashe ‘yan mata fiye da dari biyu suka yi gaba da su. Wannan lamarin ya harzuka al’ummar duniya inda kasashe daban daban suka yi tur da lamarin tare da yin zanga-zanga.

Duk da cikarsu shekara daya a hannun ‘yan ta’adan duniya bata manta dasu ba saboda dalilinsu ya sa Muryar Amurka ta shirya taro na musamman.

Jiya Talata Muryar Amurka ko VOA ta shirya wani taro na musamman a hedkwarta dake Washington DC, inda aka yi juyayi akan ‘yan matan dari biyu da goma sha tara da har yanzu suna hannun 'yan ta'adan Boko Haram.

Yayinda take jan akalar taron Jamila Fagge, ma’aikaciyar Muryar Amurka, tace “na yi murna matuka mun kasance a wannan ranar domin mu nuna damuwarmu”

Cikin wadanda suka halarci taron har da wata Patience Bulus wadda tana cikin ‘yan matan da aka sace amma ta sallake rijiya da baya tare da wasu. Yanzu su goma sha daya suna nan Amurka suna cigaba da karatunsu.

‘Yar Majalisar wakilan Amurka ta jam’iyyar Democrat daga jihar California Karen Bass da ta halarci taron tace lamarin ya tayar da hankalin duniya.

XS
SM
MD
LG