Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cika Shekara ‘Daya Da Sace ‘Yan Matan Chibok


Une manifestation tenue dimanche 12 avril 2015 à Washington, Etats-Unis, pour réclamer la libération de 276 lycéennes enlevées un an plus tôt à Chibok au Nigéria
Une manifestation tenue dimanche 12 avril 2015 à Washington, Etats-Unis, pour réclamer la libération de 276 lycéennes enlevées un an plus tôt à Chibok au Nigéria

Zababben shugaban kasar Najeriya mai jiran gado Janal Muhammadu Buhari, yace bazai yi alkawarin cewa gwamnatin sa tana da tabbacin samo ‘yan matan da kungiyar Boko Haram ta sace guda 219 a garin Chibok shekarar da ta wuce.

A cikin wani bayani da yayi jiya Talata, lokacin da ake cika shekara ‘daya da sace ‘yan matan na Najeriya.

Janal Buhari ya ‘kalubalanci gwamnati mai ci a yanzu da rashin kokarin neman ‘yan matan, inda yace gwamnatin sa ba zatayi ba abinda wannan gwamnatin tayi ba. ya kuma ce, a ranar daya karbi ofis kungiyar Boko Haram zata san iyakacin ‘karfin mu.

Kungiyar kare rajin ‘dan Adam ta duniya Amnesty Internationl, tace mayakan Boko Haram sun sace mata a kalla dubu biyu a Najeriya, tun lokacin da kungiyar ta fara a shekarar ta 2014, tana kuma tilastawa yawancin matan bauta ta ‘bangaren jima’i da mai dasu wani ‘bangare na mayakanta.

Kungiyar Amnesty ta fitar da wani rahoto a jiya Talata, da yake nunin yadda kungiyar Boko Haram ke mai da mata da mazan da suka sace a garuruwan da suka kwace. An hada rahotan ne bisa amfani da shaidun ido guda 200, da suka ga yadda aka kashe mutane sama da 5,000 a kudu maso gabashin Najeriya, tun daga farkon shekara ta 2014 zuwa yanzu.

Amnesty tace, ana tilastawa maza manya da kanana zama mayakanta ko a kashe su, su kuma mata da ‘yan matan da ake sace ana tilasta musu auren mayakan kungiyar, yin jima’i dasu, dama koya musu hanyoyin yaki don taimakawa mayakan.

Wata shaidar gani da ido ta bayyana yadda aka tilasta mata kai hari garin su, ta kuma ce mayakan na kwanciya da ita ba sau ‘daya ba sau biyu ba. shaidun dai sun nuna yadda ake jefe duk wani ko wata da suka ki zama mayakan na kungiyar.

XS
SM
MD
LG