Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace Karin Mata A Jihar Borno


Wasu daga cikin dalibai mata da aka sace a Chibok wadanda suka tsere
Wasu daga cikin dalibai mata da aka sace a Chibok wadanda suka tsere
Jami’an yanki da kuma mutanen wasu kauyuka a yankin arewa maso gabashin Najeriya sun ce wasu ‘yan bindigar da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun sace mutane masu yawa a Jihar Borno.

Suka ce ‘yan bindigar sun sace mutane fiye da 90, akasarinsu mata, manya da kanana, a hare-hare kan kauyuka a karshen mako.

Majiyoyin sun fada yau talata cewa an kai hare-haren ne kan kauyuka kimanin kilomita 100 daga Maiduguri, babban birnin jihar.

Har yanzu ba a ji ta bakin gwamnati ba, haka kuma babu wanda ya dauki alhakin satar mutanen.

Kungiyar tsagera ta Boko Haram ta kai hare-hare masu muni a wannan yankin cikin shekaru biyar da suka shige a bisa ikirarinta na neman kafa kasar Islama a arewa maso gabashin Najeriya.

Har yanzu babu labarindalibai mata 200 da aka sace daga Chibok a watan Afrilun da ya shige.
XS
SM
MD
LG