Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Iya Yin Zanga-Zanga a Abuja Kan 'Yan Matan Da Aka Sace


Masu zanga-zanga a Abuja
Masu zanga-zanga a Abuja
Sefeto janar na ‘yan sandan Najeriya, M.D Abubakar yace masu yin zanga-zanga kan ‘yan makaratar matan Chibok da aka sace suna da damar yin zanga –zangar su ta lumana ba tare da an tsangwamesu ba.

Wannan furuci ya biyo bayan sanarwar da kwamishina ‘yan sandan Abuja ya bayar cewa ba’a yarda a sake yin wani zanga-zanga dangane da ‘yan matan da aka sace ba.

Tuni masu gudanar da wadannan zanga-zanga suka shigar da kara a babban kotun Abuja suna kalubalantar jawabin kwamishina ‘yan sandan Abuja,inda suke so kotu ta tabbatar masu ko kwamishina,nada hurumin hanna su a bisa doka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:53 0:00
Direct link
XS
SM
MD
LG