Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Samsung Ya Kaddamar Da Sabuwar Wayar Galaxy S9


Kamfanin Samsung ya bayyana sabuwar wayarsa ta Galaxy S9 ranar Lahdi, inda ya baiwa kafofin sadarwa muhimmacin da zummar janyo hankulan matasa duk kuwa da ja bayan da ake fuskanta a kasuwar wayoyin zamani.

Yayin da aka hangen kasuwar wayoyin zamani zata tsaya cik ko kuma ta samu koma baya, masu sayar da wayoyin na mayar da hankali ne kan sabbin fasahar, da aka kirkira da zata karfafawa masu amfani da wayoyin, da karfafamu gwiwar sake wayoyinsu kafin lokutan da suka tsara yin wannnan sauyi.

Samsung ya kaddamar da Galaxy S9 ne a wajen taron kolin kayayyakin fasaha da aka gudanar a birnin Barcelona, domin janyo hankulan dubban manema labarai ta hanyar nuna musu irin rawar da katafaren kamfanin ya taka wajen kirkirar wannan sabuwar fasaha.

A sabuwar wayar an ‘kara karfin kamarar ‘daukar hoto, da kuma sabunta fasahar yin magana, inda ta hanyar magana ake baiwa waya umarni. Allon sabuwar wayar Galaxy S9 yafi girman na tsohuwar wayar Galaxy S8.

Yayin da kamfanin Samsung ke ci gaba da tabbatar da tazara kan abokan karawarsa irin su Apple, kamfanin na fuskantar kalubale daga kamfanonin da suka fito daga kasashe irinsu, Indiya da China da sauran kasasehn yammacin Turai, wadanda ke fitar da wayoyin zamani masu rahusa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG