Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Bayyana Dalilan Sa Na Auren Mata Biyu A Rana Guda


Wani mutun da aka sani da suna Ejindu ya auri mata biyu a rana guda a wata cocin Pentecostal dake Agbala Amangudu a jihar Abia. Sunan Matan Oyediya da Ebere.

Mujallar Daily Post ce ta wallafa labarain kuma wannan ba shine karo na farko da wani ke aurar mata biyu a lokaci guda ba, an samu wani rahoto da ya shaida cewa wani mutun dan shekaru 30 mai suna Isiyaka Dahiru, ya bar mutane da sambatu a lokacin da ya auri mata biyu a lokaci daya a jihar Nassarawa.

Har’ila yau akwai wani Omamuzo Utomajiri, mai shekaru 39 a karamar hukumar Isoko, ta kudu a jihar Delta, da ya auri matansa biyu a lokaci daya, yana mai cewa yayi hakan ne domin ya tabbatar da cewa bashi da wata damuwa kuma ya hana kanshi neman wadansu matan a waje.

Ejindu ya auri matansa biyu a coci a ranar lahadi bayan sun gudanar da bikin su na gargajiya ranar asabar a gaban ‘yan uwa da abokanan arziki.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG