Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekarar 2017 Na Cike Da Abubuwan Bazata


Shekarar 2017, shekara ce mai dauke da abubuwa da baza’a taba mantawa da suba, a tarihin karni na ashirin da daya 21. A karon farko da yanar gizo ta taka muhimmiyar rawa wajen ruruta labaran karya da basu da makama.

Kana ‘yan kutse sun yi amfani da kafofin yanar gizo, wajen satar bayanan sirri, ba kawai na mutane ba harma da na manyan kamfanoni a fadin duniya. Kamfanin Yahoo, ya fuskanci makamanciyar wannan matsalar, inda aka sami damar shiga cikin asusun kamkanin fiye da mutane billiyan daya a duniya.

Haka wani babban asibiti dake kasar Amurka, sun fukanci matsalar satar bayanai da aka dauki bayanan marasa lafiya na asibitin. Da dama daga cikin kamfanonin nan sun kashe zunzurutun kudade wajen shawo kan matsalar.

Wayoyin hannu da dama a fadin duniya sun fuskanci barazana, wajen aika wasu cututtuka dakan iya cutar da wayoyin “Virus” Kasar India ita ce kasar da ta fi kwararan matakan tsaro wajen ajiyar bayanan sirri na kamfanoni da mutane a fadin duniya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG