Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alfarma Koda Ta Aure Ce Sai Ka Ji Ance Ai Mawaki Ne - Inji Hyber Dan Baba


Abdulrashid Idris AKA Hyber dan Baba.
Abdulrashid Idris AKA Hyber dan Baba.

Babban abin damuwa ga masu harkar wakar hip-hop bai wuce yadda da dama idan munje neman wata alfarma ko ta aure ko makamancin haka sai a ce ai mawaki ne- inji matashin mawakin hip-hop Abdulrashid Idris wanda aka fi sani da Hyber dan Baba.

Ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA inda ya ce wakokinsa na fadakarwa ne mussaman ga matasa da ke da dabi’u marasa kyau- misali a wata wakarsa ta Dan-Baba.

Matashin ya bayyana cewa yana wa’azantar da matasa ‘yan daba, ko masu danfara inda ya yi wa ‘yan danfara lakani da ‘dan babadomin al’umma su sani tare da fadakar da ‘yan damafara domin su shiryu.

Dag karshe ya ce mafi yawan wakokinsa dai wa’azi ne, a cewarsa waka wata kafa ce ta isar da sakonnin cikin sauki. Dan baba ya ce burinsa wakokinsa su ilmantar tare da samun daukaka a fadin duniya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG