Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirgegiyar Damisa Tayi Kalaci Da Uwargijiyarta


Jiya da safe ne rahoto ya fito daga gidan ajiyar namun dawa Zoo, na ‘Saouth Lakes Wild Animal Park’ a kasar Birtaniya, wanda wata shirgegiyar Damisa tayi kalaci da ma’aikaciyar gidan. Sara McClay, mai shekaru 24, da haihuwa ta kasance mai renon namun daji a gidan na wasu tsawon shekaru.

Rahotannin sun bayyanar da cewar ma’aikaciyar, tana kokarin bama damisar abun karyawa da safe ne, wanda ajalinta yazo a lokacin da Damisar, tayi kukan kura akanta.

An dauki Sara, da jirgin sama mai tashin angulu zuwa asibiti, amma batayi rai ba, a cewar mahukuntan gidan Zoo din, wannan wani abune da za’a tsanannta bincike don gano dalilin abkuwan hakan. An bayyanar da mamaciyar da cewar, mace mai sha'awar namun daji matuka.

Sun kara da cewar, a dai-dai lokacin da abun ya faru, babu mutane masu zuwa kallo, don haka kada mutane su shiga cikin damuwa. Damisar dai na daya daga cikin damisoshi hudu, mafiya hadari da ake da su a gidan Zoo din.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG