Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba'a Bar Kasashen Afrika A Baya Ba, Wajen Kere-Keren Mutunmutumi


Taron matasa masu hazaka daga kasashen Saharar Afrika, suna cigaba da gudanar da gasa a tsakanin su, wajen kirkirar mutunmutumi a babban birnin Darkar kasar Senegal.

Mahalarta gasar dai ‘yan makarantar sakandire ne a baki dayan kasashen da suka shiga gasar. A cewar kungirar da ta dauki nauyin wannan gasar, sun hada wannan gasar ne, don nuna ma gwamnatocin kasashen Afrika, irin matasa da baiwar da Allah yayi musu.

Koda hakan zai basu karfin gwiwar taimakama matasan, musamman a bangaren kimiyya da lissafi, haka tsarin da suke da shi yana ba matasa damar haduwa da wasu matasan masu wata basirar don karama juna sani.

Shugaban taron Sidy Ndao, yace taken wannan shekarar shine, ‘Kaya ‘yan Afrika’ da zummar ganin yadda mutunmutumi zai taimaka wajen ganin tattalin arzikin kasashen Afrika ya bunkasa.

Sai ya kara da cewar, mafi akasarin kasashen da suka cigaba a duniya, kamar su Amurka, suna dogaro ne da abubuwan da suke kerawa, amma kasashen Afrika an barsu a baya, yana ganin cewar idan kasashen Afrika zasu dinga dogaro da kansu, musamman da irin basirar da Allah yayi ma ’yan kasashen.

To babu shakka kasashen Afrika, zasu zama abun koyi a duniya, babu dalilin dai zai sa kasahen Afrika su dinga koyi da wasu kasashe, tunda akwai duk abun da ake bukata na cigaba a kasashen Afrika.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG