Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Ayi Gwanjon Jakar Da Aka Fara Zuwa Duniyar Wata Da Ita


An bayyanar wata jaka, daya daga cikin abubuwan farko da aka fara tafiya duniyar wata dasu, kimanin shekaru daruruwa da suka gabata. An tabbatar da cewar wannan jakar itace abu guda yada da yanzu ake da ita a hannu.

Kuma jakar na dauke da wasu duwatsu da aka debo, Mr. Neil Armstrong, shine mutun na farko, da ya fara zuwa duniyar wata a tarihin duniya. An shiryar da yin gwanjon jakar a ranar 20 ga watan Yuli, inda ake sa ran jakar zata iyayin tsada da kankai dallar Amurka milliyan $4M kwatan kwacin naira billiyan daya da milliyan dari biyar.

Ga dukkan alamu, jakar ta taimaka matuka a yayin wannan tafiyar da akayi a kumbo ‘Apollo 11’ domin da ita akayi amfani wajen kawo samfur na kasar dake sararrin samaniya. Ganin wannan jakar da akaje wajen da mutun bai zai taba tunanin zuwaba, wanin abun ban sha’awa ne da tarihi.

Karanta labarin zuwa duniyar wata, ba daya yake da mutun ya taba wannan jakar da aka ziyarci duniyar watan da itaba. Don haka wannan wani abun tarihi ne da za’a nunama duniya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG