Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'ar 'Harvard' Zata Karrama Matashin Mawaki Da Digirin Farko


Matashin Mawaki
Matashin Mawaki

Wani dalibi dake kokarin kammala karatun digirin farko a jami’ar Harvard, dake kasar Amurka. Zai mika aikin karshe don samun takardar shedar kammala karatu a jami’ar da tafi kowacce jami’a girma a duniya.

Obasi Shaw, mai shekaru 20, ya rera wakoki 10, mai taken ‘Sabuwar Zuciya’ matashin dai ya bayyanar da samun wannan sha’awar ta waka, a irin rubuce-rubuce da ya keyi na labarum almara.

Aikin matashin da suka hada da wakoki 10, suna daga cikin aiki da ba’a taba samun irin shi ba, a tarihin jami’ar Harvard tun bayan kafata da akayi, a shekarar 1636, kimanin shekaru 380 da suka gabata.

Duk wani dalibi da zai kammala karatun digiri da yake da bukatar kammalawa da lambar yabon karramawa, sai yayi rubuce-rubuce, wanda zai tabbatar da kwarewar dalibin a fannin shi.

Dalibin da bai da bukatar hakan, ba sai yayi rubuce-rubucen ba. Amma Obasi, ya zabi rera wakoki 10, a matsayin aikin shi na karshe don samun lambar yabo mafi girma, daga jami’ar Harvard.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG