Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Matasa Sun Gano Karin Hanyoyin Amfana Da Gashin Kaji


Shekaru da dama da suka wuce, ana sarrafa gashin kaji, wajen amfani da dama. Wasu kadan daga cikin abubuwan da akanyi amfani da gashin shine, akanyi rigunan sanyi, katifa, filo, bargo, kana akanyi amfani da gashin wajen kayatar da wurare.

Sau dayawa mutane kan yanka kaji, da daukar naman kajin batare da amfana daga gashin kajin ba. Yanzu haka dai wasu dalibai dake gudanar da wani bincike, mai zurfi a matakin digirin-digirgir a jami’ar birnin Birtaniya.

Sun gano wata hanyar amfani da gashin kaji, wajen samar da wasu kayan amfanin yau, da kullun na gida. Binciken su ya nuna musu wasu hanyoyi da za’a iya sarrafa duk wani gashin kaji, tsuntsaye da ke da fiffike.

Tsuntsayen dai, Allah yayi musu wannan gashin ne, don samun kariya daga yanayin zafi, sanyi da duk wani abu da kan iya cutar da su. Yanzu haka suna kokarin samar da hanyar da mutane zasu dinga amfani da gashin wajen samar da aikin yi da sana’a ga mutane.

Wasu sinadarai da suke amfani da su wajen sarrafa gashin, don samar da kaya da suka hada da robobin kayatar da daki, kayan wasan yara, da dai makamantan su. Amfani da gashin kaji na da sauki wajen sarrafawa, don rashin nauyin shi, zai bada damar amfani da sinadarai kadan, don samun abu mai yawa cikin kankanin lokaci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG