Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

kelechi Iheanacho Ba Zai Sami Takawa Najeriya Leda Ba


Daga dukkan alamu Kelechi Iheanacho, dan kungiyar kwallon kafa na Manchester City, ba zai samu zuwa Brazil, ba domin takawa Najeriya leda, a gasar Olympic na bana.

Kelechi Iheancho, dan shekaru 19, da haihuwa sunan sa na cikin ‘yan wasa 35, da zasu wakilci Najeriya, a gasar Olympic, wanda za’a gudanar a Rio de Janeiro, ta kasar Brazil.

Manchester City, dai na bukatar Kelechi, domin ya buga mata wasanin da zata yi gabanin a fara kakar wasa.

Matashin dan wasan yace duk wanda kasar sa ke bukatar shi domin ya buga mata wasa tilas ne mutun yayi farin cikin haka, ya kara da cewa ya rage tsakanin kungiyar Manchester da Najeriya.

XS
SM
MD
LG