Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gurfanar Da Likitan Kai Daukin Gaggawa Elena Duta Da Yin Sakacin Ceto Rayuwar Patrick Ekeng


Yanzu haka ana nan ana fafata wasan farko na matakin kwata final na gasar kwallon kafa na cin kofin nahiyar turai tsakanin kasashen Poland da Portugal, kasar Poland ta sami kaiwa matakinne bayan ta doke kasar Switzerland a matakin ‘yan sha shidda da ci biyar da hudu a bugun Fenariti bayan da wasan su ya karkare a kunnen doki da ci daya da daya.

Ita kuma Portugal ta sami tsallakewa ne biyo bayan kashin da taba Croatia da ci daya mai ban haushi.

Bayan fitar da kasarsa daga gasar cin kofin nahiyar turai, dan wasan gaba na kasar Sweden Zlatan Ibrahimovic ya bayyana aniyarsa ta komawa kulob din Manchester united ta Ingila, Ibrahimovic dan shekaru talatin da hudu ya bayyana yin murabus daga yiwa kasar sa wasa bayan wasanni 116 da ya buga mata.

Masu shigar da kara a kasar Ramaniya sun gurfanar da wani likitan kawo daukin gaggawa a gaban kuliya bisa zargin musabbabin mutuwar dan wasan kasar Kamaru Patrick Ekeng dan shekaru 26, wanda ya yanke jiki ya fadi a lokacin da yake bugawa kungiyar su wasa a watan da ya gabata.

Masu shigar da karar sun ce likitan yaki yayi kokarin ceto rayuwar dan wasan a lokacin da yake cikin motar daukar marasa lafiya a hanyarsu ta zuwa asibiti, ina a can asibitin likitocin suka yi kokarin su amma bayan sa’oi biyu aka bayyana mutuwar sa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:59 0:00
Direct link

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG