Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Wasu Matasa Masu Yiwa Mata Fyade


Rundunar ‘yan Sandan Jihar Akwa Ibom, ta cafke wasu matasa uku da suka shahara wuri yiwa ‘yan mata fyade a Uyo.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar, ASP Cordelia Nwawe, ta nuna matasa ga manema labarai a hedkwatar rundunar dake Uyo, matasan sun hada da James Etim, dan shekaru 24, Charles Essien, 27, da Utebe Archibong dan shekaru 29.

Kakakin ‘yan Sandan tace matasa na amfani da keke Napep, ko kuma a daidaita sahu wajen gudanar da mummunar aikin da suke aikatawa ‘yan mata,

Wata ‘yar jami’ar Uyo, da suka dauka ce ta kai labarin ga ‘yan Sanda, duk da barazanar da suka yi mata bayan da suka sa ta rantse da cewa zata mutu idan har ta fada wa wani abuinda ya faru, wanda daga bisani bayan samu labarin sai ‘yan Sanda suka yi masu kwantan bauna suka cafke su.

Da suke amsa laifin su matasan sun ce basu san adadin matan da suka yiwa fyade ba.

Rundunar ‘yan Sandan tace da zaran ta kamala bincike za’a gurfanar dasu a gaban kotu.

XS
SM
MD
LG