Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Matasa Sun Bukaci Majalisar Dattawa Da Ta Wakilai Su Rage Shekarun Shiga Takara


Kungiyar matasa mai suna youth Initiative for advocacy and advancement da wasu kungiyoyin matasa sun kai ziyara a majalisar tattawa da kuma majalisar wakilai inda suka bukaci a rage yawan shekarun takara daga shekarua majalisar dattawa daga shekaru 35 zuwa 30, a majalisar wakilai kuma daga shekaru 30 zuwa shekaru 25.

Wannan bukarta a cewar daya daga cikin matasan mai suna Maryam Laushi, ta bayyana cewa suna ganin ya kamata a fara damawa da su domin kuwa, matasa na taka rawar gani a harkokin ciyar da kasar gaba. Matasa na daga cikin kaso mai yawa cikin wadanda ke rike da kujerun gwamnati a wannan sabuwar gwamnati.

Ta kara da cewa hatta masu rubutawa manyan kasidu da sauran takardun da suke karantawa a wuraren tarurruka da tsarin gudanar da ayyukan kasa matasa ne, kuma anyi amfani da matasa soasai a lokacin yakin neman zaben wannan gwamnati, dan haka ya kamata a dama dasu wajan mulkin kasar domin ciyar da kasa gaba.

Matashiyar ta ce, matasa nada zafin jini kuma zasu iya yin duk wani abu da magabatan su ke yi domin gina kasa, domin haka a cewarta hada kai da matasa wajan tafiyar da al’amurran kasar zai taimaka wajan ciyar da Najeriya gaba.

A yanzu haka dai yunkurin da matasa suka yi, ya kaiga majalisar wakilai kuma da alamu anyi karatu na biyu yanzu haka ana jiran karau karo na uku ne domin ganin yadda za’a iya cimma kudirin matasan.

Saurari rahoton a nan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Direct link

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG