Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Labarai

Laraba 20 Yuni 2018

Calendar
2018 2017 2016 2015
Janairu Fabrairu Maris Afrilu Mayu Yuni Yuli Agusta Satumba Oktoba Nuwamba Disamba

Kamfanin Apple ya fitar da wata sanarawa a ranar Laraba data gabata cewar zai dauki wani sabon mataki na toshe haryar da jami’an bincike ke amfani da ita wajan samun bayanai yayin da suke gudanar da binciken kwakwab akan wanda ya aikata lafiya, lamarin da ake tunanin zai sake haifar da takaddama akan ko kanfanoni na taka rawar gani wajan taimakawa yaki da aikata mugann laifuka.

Apple ya bayyana cewa sauyin da zai kaddamar wani yunkuri ne na inganta wayar da kamfanin ke yi a duk wasu lokuta da ake kira update a turance, wayar zata rufe kanta awa guda bayan mai wayar ya kammala amfani da ita.

Wani shahararren kamfani mai mazauni a jihar California ta Amurka “Boring Company” na gab da kammala shirin sa na sufuri wanda zai iya daukar motar matafiyi don kai shi wani gari, tsarin wanda aka shirya a cikin karkashin kasa mai kimanin kilomita 3.2 cikin zurfin kasa.

Shirin zai dauki mutun da motar sa, kuma yana gudun famfalaki wanda hakan zai kawo karshen matsalar cinkoson ababen hawa a cikin manya manyan garuruwa.

Za'a fara gwajin sabon tsarin a jihar ta California, kamfanin wanda yake daya daga cikin bangaren kamfanin Tesla masu kera motoci masu amfani da hasken rana na kasar Amurka, da jirgin nan mai shiga cikin sararrin samaniya na SpaceX.

Yi Lodin Kari..

XS
SM
MD
LG