Shirin mu na matasa da siyasa na wannan mako ya samu bakuncin Injiniya Rufa’I Dagumawa wakili a kungiyar Arewa Youth Assembly Gammayar, kungiyoyin matasan Arewacin Najeriya.
A shirin mu na mata da sana'a yau Dandalin VOA ya dira jihar Kaduna, inda wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir, tayi hira da Zainab Lawal Nasarawa, mai sana’a Mocktail, wato samar da lemo ta hanyar sarrafa kayan marmari.
Matashi kwamared Aliyu Samba, shugaban kungiyar "Mu Kawar Da Bara Movement", da ta Almajiri Child Initiatives ya ce wani gangami fadakarwa da suka gudanar a jihar Kaduna ya ja hankalin gwamnonin jihohin Arewa wajen waiwayar matsalar bara.
Hussaina ta ce ta fara sana’ar kayan kamshin na Sizzle and Spice, kimanin shekaru biyar da suka gabata, inda ta ce ta kan yi adadi da dan dama kuma ya danganta da yadda ake bukata.
Aikace-aikacen bil adama da suka hada da rage dazuka da bunkasar birane, ya sa dabbobin suna kai hari kan gonaki don neman abinci, suna lalata amfanin gona da darajarsu ta kai ta miliyoyin daloli.
A kwanaki baya ne dai labari ya mamaye kafofin sada zumunta na cewa shahararren jarumin fina-finan Hausa Rabiu Rikadawa ya yi hadari ya rasu, lamarin da ya janyo masoyansa suka shiga cikin dimuwa da damuwa. Amma jarumin ya fito ya karyata hakan.
Yi Lodin Kari..