A wani wassanin da ake yi a kowace farkon shekara a kasar Peru, mutanen da suke da tsama a tsakaninsu suna haduwa su ba hammata iska wato su dambace domin kece rainin da ke tsakaninsu sannan su yafewa juna a cikin sabuwar shekarar.
Manyan ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG- Paris Saint-Germain sun yi bankwana da shekarar 2017 da buga tamaula kan filin da aka shimfida kan ruwa, yayin da kungiyar ke wasannin sada zumunci a Qatar a wannan makon.
A wannan wurin cin abincin da ke India, 'yan matan mutum-mutumi ke aikin raba abinci ga kwastomomi kuma su dawo su kwashe kwanukan bayan an kammala.
Wannan asibitin zamani da aka bude shi musamman don rakuma, an kafashi ne domin raya al'adun yankin inda ake gasar tseren rakuma. Asibitin na da gadajen duba rakuma 20 da wurin tsere don taimakawa rakuman su samu sauki.
Wani dan Burtaniya, Tom Morgan ya makalawa kujera balan-balan guda 100 da ya hura sannan ya hau ta yi sama da shi har ya yi tafiyar kilomita 24 cikin sa'o'i 2. Tom yana cikin wata kungiyar masu yawon bude ido da ke kokarin rage damuwa da samar da jin dadi a duniya.
Wata mace da aka haifeta ba mahaifa ta haihu sakamakon wata dubarar likitoci da ka iya magance matsalar rashin haihuwa a mata
A kasar da aka haramtawa mata shiga wasannin motsa jiki, wadannan 'yan mata sun koma koyon kokawar karate domin kare kai.
"Terzo Millennio" aka yi wa sabuwar motar kampanin Lamborghini lakabi. Motar tana dauke sabuwar fasahar inji kuma ta yi kama da kunbo mai daukar 'yan sama jannati.
A yayin da aka doshi bukukuwan Kirsimeti a Amurka, an fara kawata tagogi, musamman na kantuna da shaguna, a birnin New York, da abubuwa na jan hankulan jama'a domin su shiga irin wadannan kantuna su yi sayayya, ko jan ra'ayinsu game da wani batu.
Wanzamai sunyi bikin nuna al'adunsu da martabansu a Jamhuriyar Nijar.
Yi Lodin Kari..