A kasar da aka haramtawa mata shiga wasannin motsa jiki, wadannan 'yan mata sun koma koyon kokawar karate domin kare kai.
"Terzo Millennio" aka yi wa sabuwar motar kampanin Lamborghini lakabi. Motar tana dauke sabuwar fasahar inji kuma ta yi kama da kunbo mai daukar 'yan sama jannati.
A yayin da aka doshi bukukuwan Kirsimeti a Amurka, an fara kawata tagogi, musamman na kantuna da shaguna, a birnin New York, da abubuwa na jan hankulan jama'a domin su shiga irin wadannan kantuna su yi sayayya, ko jan ra'ayinsu game da wani batu.
Wanzamai sunyi bikin nuna al'adunsu da martabansu a Jamhuriyar Nijar.
Wasannin 'Yan Bori a Jamhuriyar Nijar
Mutane sun dauki hoton wani karamin jirgi da ya sauka ba shiri akan titin mota a jihar Florida. Matukin jirgi bai ji rauni ba inda ya shaida cewa ya samu matsalar injin ne bayan da ya taso daga filin jirgin saman Clearwater Airpark.
Wan mai kirkira dan Burtaniya, Richard Browning, ya shiga kundin tarihin duniya a wanda ya kirkiro da riga mai injin tashi da ta fi kowacce gudu a duniya.
A Lithuania an yi gasar shekara-shekara na sarauniyar gashi da ta tattaro 'yan mata 100 daga sassan kasar. Wata matashiya 'yar shekaru 21 ita ta lashe gasar inda gashinta ya kai tsawon mita 1.6.
A Indonesia mutane na kokarin mayar da manya-manyan kifayen sperm whale guda 12 wadanda suka makale a gabar tekun Tsibirin Sumatra, bayan da suka biyo igiyan ruwa sannan suka kasa komawa cikin teku saboda girmansu.
An yi shagalin abinci da jibgegen kifin whale na farko a Japan da nufin bunkasa cin naman kifin a kasar.
A Yola, sha'awar tufafin ma'aikatan banki ya kai wani matashi amfani da kwot a wajen sana'arsa ta sayar da kayan marmari.
Yi Lodin Kari..