A Indonesia mutane na kokarin mayar da manya-manyan kifayen sperm whale guda 12 wadanda suka makale a gabar tekun Tsibirin Sumatra, bayan da suka biyo igiyan ruwa sannan suka kasa komawa cikin teku saboda girmansu.
An yi shagalin abinci da jibgegen kifin whale na farko a Japan da nufin bunkasa cin naman kifin a kasar.
A Yola, sha'awar tufafin ma'aikatan banki ya kai wani matashi amfani da kwot a wajen sana'arsa ta sayar da kayan marmari.
Wani dan Canada, Kurt Sorge ya zama mutum na farko da ya lashe gasar wasa da keke akan tsaunuka na Red Bull sau uku. An yi wasannin ne a wani yankin Jihar Utah mai kayatarwa inda gwanayen suka yi wasannin ganganci yayin da suke gudu da keke.
A Birnin Washington DC, daruruwan mutane sun yi tseren shekara-shekara sanye da takalma masu tsini da ake gudanarwa a talatar da ke gab da shagalin Halloween.
Duk da yadda wutar daji ta kone gidaje a jihar California wani mai raba wasiku bai fasa kai wasiku ba
Dattijai a Birnin Johannesburg suna yakar tsufa ta hanyar damben boxing da ke basu damar motsa jiki don rage radadin tsufa.
Zai iya girka duk irin abinci da mutum ke bukata ta hanyar ba shi umarni a manhajar wayar hannu.Idan kana kan hanyar zuwa gida kana iya kunnashi ta waya don ya fara girki kafin ka iso kuma babu wani hadari a ciki.Bugu da kari, har da yin wanke-wanke da gyara waje bayan girki.
Yi Lodin Kari..