A Yola, sha'awar tufafin ma'aikatan banki ya kai wani matashi amfani da kwot a wajen sana'arsa ta sayar da kayan marmari.
Wani dan Canada, Kurt Sorge ya zama mutum na farko da ya lashe gasar wasa da keke akan tsaunuka na Red Bull sau uku. An yi wasannin ne a wani yankin Jihar Utah mai kayatarwa inda gwanayen suka yi wasannin ganganci yayin da suke gudu da keke.
A Birnin Washington DC, daruruwan mutane sun yi tseren shekara-shekara sanye da takalma masu tsini da ake gudanarwa a talatar da ke gab da shagalin Halloween.
Duk da yadda wutar daji ta kone gidaje a jihar California wani mai raba wasiku bai fasa kai wasiku ba
Dattijai a Birnin Johannesburg suna yakar tsufa ta hanyar damben boxing da ke basu damar motsa jiki don rage radadin tsufa.
Zai iya girka duk irin abinci da mutum ke bukata ta hanyar ba shi umarni a manhajar wayar hannu.Idan kana kan hanyar zuwa gida kana iya kunnashi ta waya don ya fara girki kafin ka iso kuma babu wani hadari a ciki.Bugu da kari, har da yin wanke-wanke da gyara waje bayan girki.
Yayin da mahaukaciyar guguwar teku mai suna Ophelia ta ratsa ta yankin Wales da ke Burtaniya wasu sun fita kallo.
Tun daga lokacin ya hadu da masu wannan harkar har ma da yin baja kolin nunin zane-zanensa da ke bayyana ire-iren kalubalai da tsangwama da rashin kula a rayuwa. Yana da burin yin aure watarana da kuma haihuwa kuma yana fatan bude wajen zane-zane inda zai iya koyar da wasu yara masu nakasa.
Yi Lodin Kari..