Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
16x9 Image

Mahmud Lalo

Mahmud Lalo haifaffen garin Jos ne da ke jihar Pilato amma dan asalin jihar Kano. Ya kammala karatun firaimarinsa a makarantar Al –Iman da ke Dogon Dutse a Jos.

Daga nan ya dangana zuwa makarantar sakandaren kimiyya ta kwana wato Science Toro da ke jihar Bauchi. Bisa wasu dalilai, ya sauya makaranta, inda ya koma Government Secondary Jos (GSS Jos) – wacce daga baya ta koma Sardauna Memorial College.

Bayan kammala karatun Sakandare, ya garzaya zuwa Jami’ar Bayero da ke jihar Kano inda ya nazarci fannin Diploma in Social Policy and Administration – wato tsare-tsare a fannin sha’anin jama’a da shugabanci a tsangayar nazarin halayyar dan adam 2000.

Daga nan, sai ya samu gurbin karatu a tsangayar nazarin aikin jarida ta Jami’ar Bayero inda ya kwashe shekaru sama da hudu yana karatu.

Ya yi wa kasa hidima (NYSC) a yankin Jos ta Kudu da ke jihar Pilato a makarantar nazarin aikin talbiji ta NTA College inda ya samu damar karin ilimi a wurin gogaggun ‘yan jarida irinsu Eugenia Abu.

Bayan kammala aikin yi wa kasa hidima, ya fara samun aiki da kamfanin Media Trust a Abuja, babban birnin Najeriya, kamfanin da ke wallafa jaridun Daily Trust, Weekly Trust, Aminiya, Sunday Trust da mujallar Tambari.

Daga nan ya koma aiki da Radio France International (RFI) Hausa Service a jihar Legas da ke kudancin Najeriya.

Bayan kwashe kusan shekaru uku a Legas, ya samu aiki da British Broadcasting Corporation (BBC Hausa Service) a Abuja.

A gidan rediyon na BBC, ya samu damar zuwa kwalejin aikin jarida ta BBC da ke Dakar, babban birnin Senegal domin karo ilimin aikin jarida, musamman a fannin ilimi kan sabbin kafafen yada labarai na zamani.

Yanzu haka, ya na aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka VOA a Washington, inda yake hada rahotanni, ya gyara ya kuma gabatar da labarai a sassan yada labarai daban-daban.

Shi ne ya sauya fasalin shirin Duniyar Amurka yake kuma gabatarwa, shirin da ya kunshi al’adu, diflomasiyya, nishadi, kiwon lafiya, siyasa a Amurka, wanda yake gabatarwa a duk ranar Juma’a.

Ya kan tsara ya kuma jagoranci “Shiri na Musamman” na radiyo a ko wane mako, wanda ke tabo batutuwa daban-daban a sassan duniya, musamman a yankunan Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi. Kuma edita ne na shafin yanar gizon Sashen Hausa na Muryar Amurka da sauran kafafen sada zumuntar sashen.

Baya ga haka, yana daya daga cikin masu gabatar da shirin talbijin na “Taskar VOA” na talbijin, shirin da ke maida hankali kan batutuwan da suka shafi ci gaban matasa, musamman kan samun abin dogaro da kai da kuma ilimi.

Produced by Mahmud Lalo

Yi Lodin Kari..

XS
SM
MD
LG