Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
16x9 Image

Usman Ahmad

Usman Ahmad haifaffen unguwar Kabara ne a cikin birnin Kano, sannan ya girma a jihar Kaduna. Ya gama makarantar Firamare a Gawuna Primary School, ya kuma gama Sakandare a Sardauna Memorial College. Ya yi karama da babbar Difiloma ta kasa a Kwalejin Kimiyya Da Fasaha ta Kaduna Polytechnic. Ya fara koyon aikin radiyo ne daga gidan radiyon Jihar Kaduna (KSMC), sannan ya yi aiki da Mujallar FIM da ke bada labaran harkar Finafinan Hausa. Daga nan ya koma yana wallafa tasa mai suna Mujallar Sho, kafin daga bisani ya sami aiki da BBC World Service Trust a Nigeria inda ya gabatar da wani shirin matasa mai suna Ya Take Ne? Gidan radiyo da talbijin na Liberty da ke Kaduna ne wajen da yayi aiki na baya-baya da yake gabatar da shirin labarai da rahotanni na ‘Wakilan Liberty’, kafin zuwansa Sashen Hausa na Muryar Amurka da ke nan birnin Washington D.C. Yanzu haka yana gabatar da shirye-shiryen da suka hada da shirin matasa na ‘Yau Da Gobe’, ‘Nakasa Ba Kasawa Ba’ da kuma wannan shirin naku mai farin jinni na ‘A Bari Ya Huce’.

XS
SM
MD
LG