Hukumar UEFA Tana Binciken Dan Wasan Gaba Na Kungiyar PSG

Hukumar dake kula da wasan kwallon kafa ta nahiyar turai UEFA, ta na bincike kan dan wasan gaba na kungiyar PSG, Neymar, bisa kalaman da yayi bayan da Manchester United ta fidda kungiyar sa cikin gasar cin kofin zakarun turai a bana.

Neymar ya wallafa a shafinsa na sada zumunci cewar bugun daga kai sai Mai tsaron gida da alkalin wasa mai suna Damir Skomina ya yiwa Manchester United a karshen lokaci, sam bai dace ba, kuma hakan cin zarafi ne.

Alkalin wasa Damir, ya bada bugun daga kai sai Mai tsaron gidanne bayan da ya duba faifayin bidiyo mai taimaka wa Alkalin wasa, inda ya tabbatar masa dan wasan PSG Presnel Kimpembe, ya taba kwallon da hannunsa dan haka ya bada bugun da ake kira Penalty da turanci.

Neymar dai bai samu damar buga wasanni biyu da kungiyar tasa tayi da Manchester ba, sakamakon jinyar kafar sa da ya ke yi na tsawon makonni 10.

A karawar farko PSG tabi Manchester United har gida ta doketa 2-0 ita Manchester a hadu warsu ta biyu satin da ya wuce ta sha PSG kwallaye 3-1 jimillar kwallaye 3-3 sai dai United ce ta haye zuwa matakin zagayen gaba saboda kwallaye uku da ta jefa a gidan PSG (Away Goal)

Wannan binceke da akeyi kan Neymar na iya haramta masa buga wasanni har guda uku cikin gasar ta zakarun turai a shekara mai zuwa.