Sana'a Goma Maganin Mai Gasa - Umma Abdullahi

Umma Abdullahi

Umma Abdullahi – matashiya ta ce a yunkurin taimakawa kanta don zama mai dogaro da kai ne ya sa ta fara sana’ar sayar da kayan mata kamar su man girki da sabulun wanka da wanki duk a cikin gidanta.

Ta ce da taimakon yara ne take samun kasuwa inda a mafi yawan lokuta suke shiga da hajarta gidajen makwabta domin samun kasuwa, ta nan ne mutane da makwabta suka santa.

Malama Umma, ta ce daga cikin abinda ke kawo mata koma baya a sana’ar ta dai shine yawan karbar bashi daga wajen abokan sana’arta a cewarta dole sai ka bada bashi domin idan baka bayarwa toh lallai ba zaka samu ciniki ba.

Umma, ta kara da cewa a yanzu duk wani kananan bukuta na gida takan dauke wa mai gida da ma nata bukatun

Daga karshe ta ce sana’a goma maganin mai gasa hakan ce ta sa ta fadada harkar ta kuma babu abinda zata ce sai hamdala ta kuma bukaci mata da a tashi tsaye kada a jira mai gida.

Your browser doesn’t support HTML5

Sana'a Goma Maganin Mai Gasa - Umma Abdullahi