Rashin sayan hannu jari daga bangaren gwamnatin da manyan jama’ar garin na daya daga cikin abubuwan da suka hana ci gaban da ake bukata a faggen wake wake.
Wani mawakin Hip hop, Musbahu Sulaiman, ne ya shedawa wakiliyar Dandalinvoa, Baraka Bashir, a wata hira da suka yin a birnin Kano.
Sulaiman dai yace yana wakar Hip-hop da harkar Camera da editin ne domin saukakawa matasan mawaka masu tasowa in ji matashin mawakin, wanda aka fi sani da the onlyplay.
Ya ce baya ga rera waka yana harkar camera da edit ne sakamakon irin matasalar da mawaka ke fuskanta wajen hada wakokinsu, a cewarsa yana cikin mawaka kuma ya fi kowa sanin irin matsalolinsu hakance ma ta sa ya koya don jin dadin matasa.
Onlyplay ya ce babban abinda ke ci musu tuwo a kwarya bai wuce yadda al'umma da gwamnatin suka ki karfafawa mawakan gwiwa ba ta wajan sanya hannun jari a harkar waka, a cewarsa waka wata hanya ce da ke saurin kawo kudi.
Ya kara da cewa gwamanti bata nuna kulawa ga masana'antarsu kamar yadda sauran kasashen duniya ke yi wa mawaka
Musbahu ya ce babban burinsa shine ya samu ya kafa kamfanin da zai taimakawa kananan mawaka a sana’ar waka.
Your browser doesn’t support HTML5