Plateau United Ta Lallasa Jigawa a Gida

'Yan wasan kungiyar kwallo kafa ta Plateau United suna murnar zura kwallo (Hoto: Shafin Plateau United Facebook)

A ci gaba da gasar Premier League ta Najeriya, tawagar ‘yan wasan Plateau United da ke tsakiyar arewacin Naje, ta doke takwarar karawarta ta Jigawa Golden Star da ci daya mai ban-haushi.

United ta bi Jigawa har gida ne ta doke ta.

Hakan na nufin Plateau United ke ci gaba da jagorancin teburin gasar da aka fara a kwanan nan da maki 6 da kwallaye uku.

Wikki Tourist, wacce ita ke biye da Plateau United a teburind a maki 6 da kwallaye biyu, ta bi tawagar ‘yan wasan Nasarawa har gida ta lallasa da 1-0 a filin wasa na Township da ke garin Lafiya.

Ita kuwa Lobi Stars ta lallasa Delta Force ne da ci 4-0, sannan Enugu Rangers ta yi kunnen doki da Adamawa United.